Wata kishiya ta kona mijinta da amaryarsa a daren farko

Mummunan lamarin ya faru ne a jihar Kaduna dake arewacin Nigeria.

Kishiyar ta aika aika aikar ne ta hanyar kulle kofa sannan ta bude windo ta jefa wuta cikin dakin amaryar yayinda angon ke shagalin amarci da amaryarsa wanda hakan yayi sanadiyyar konewarsu gaba daya kafin jamaa su kawo dauki cikin gidan.

Bayan an ceto amarya da angon ne nan da nan aka garzaya da su zuwa asibiti inda acan ne  angon Alh. Sulaiman Kero ya dangana zuwa barzahu. 

Ita kuwa a bangaren amaryar yanzu haka tana asibiti da ranta saidai akwai raunukan wuta mai yawa ajikinta wanda ba lallai bane fatarta ta ta sake moriya mai yawa. 
Mummunan kishi yana nema zama babbar barazana ga rayuwar ma'aurata a yankin Arewacin Nigeria inda ko shekarar data wuce wata yarinya ta sheka mijinta gar lahira sakamakon kishinsa datake yi.