Shahararen jarumin fina finan Hausa ADAM A ZANGO ya sallami matarsa Ummukulsum tareda bata takardar saki acikin watan August daya gabata.
Labarin sakin ya fito ne daga mujallar FIM MAGAZINE wacce take kunshe da zallar labarai da suka shafi masana'antar Kannywood.
UmmuKulsum itace matarda Adam A zango ya aura daga kasar Cameeron kuma itace matarda ya aura ta 5, anyi aurensu ne ashekarar 2015 lokacinda ya hada mata 3 tare.
Bayan Auren UmmuKulsum ZANGO ya sallami dayar matarsa ya zauna da mata 2 kana daga bisan ya bada takardar saki ga Maryam Yola wacce ya aura bayan sunyi fim din NASS tare sai yazama matarsa 1 ta rage masa.
A watannin baya ADAM A ZANGO ya taba daukar wasu hotunan soyayya tareda UmmuKulsum ya watsa a kafafen sadarwa Kwatsam sai kuma ga labarin rabuwarsu kwanakinnan da muke ciki, Hakan yasa mutane dayawa ke mamakin dalilinsa na sakin matar tasa wacce ya bayyana soyayyarta fiyeda kowace mata daya aura a rayuwarsa.
A baya dai ADAM A ZANGO yasha fama da zarge zargen auri saki daga sassan daban daban na ma'abota kallon fina finan Hausa zarginda ya karyata sannan ya kirashi da makircin makiyansa. Saidai a yanzu kuma 'yan kallo dayawa na ganin zargin ya tabbata saboda labarin sakin UmmuKulsum wacce itace ta rage masa kuma hakan ya mayar dashi gwauro a idon duniya.
ADAM A ZANGO ya auri mata 4/5 a rayuwarsa kuma zuwa yanzu haka babu ko guda dayake tareda ita. Saidai kuma kusan kowacce mata daya aura ta akwai zuria tsakaninsu.
Ana cigaba jiran ganin wacce budurwa zai sake aure watakila daga cikin 'yan matansa na masana'antar fim ko kuma daga 'yan kallo da suke son zaman aure dashi.


