Jarumi Ali Nuhu ya samu Lambar girma ta farko a 2019

Jarumin ya bayyana irin godiya da kuma jin dadinsa ga wannan kyauta ta girmamawa da aka bashi a farkon sabuwar shekarar 2019.

Wata kungiyar #NorthernTrendz itace ta baiwa jarumin lambar yabon bayan nazari da kungiyar tayi kan kokari da jajircewar jarumin wajen ganin harkar fina finai ta cigaba ba a Nigeria kadai ba harda duniya baki daya.

Jarumai maza da mata sunyita yayata hotunan jarumin da kuma nuna murnarsu kan wannan lambar girma daya samu.