Zarcewar APC shine maslaha ga mata a Nigeria - Aisha Buhari

Uwar gidan shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari taui kira ga mata domin neman cigabansu. 

Hajiya Aisha Buhari tayi kiran ne yayin gabatarda bayani a wani dakin taro data halarta. 

Aisha tace mata dayawa suna cikin kunci, rashin ilimi da wahalhalu na rayuwa daban daban musamman a yankunan karkara. Yara dayawa basu zuwa makaranta a wasu wuraren kuma an maida mata kamar bayi su suke kowane aiki musamman noma da sauran ayyukan wahala sannan kuma ga mata masu haihuwa sunanan suma suna bukatar kulawa. 

"Saboda haka ina kira ga 'yan uwana mata da su zo su sake zabar wannan gomnati domin more shirye shiryen da akayi musu idan har an sake samun damar dawowa karagar mulki. 

Aisha ta rufe da cewa mata sune ginshikin kowace alumma don haka fitowarsu zabe shi zai taimaka samun sauki ga mazajensu da 'ya'yansu.