Wata kungiyar mata ta karrama sarkin Gombe

Wata kungiya mai fafutukar kwato 'yancin mata da yara kana ta baiwa mai martaba sarkin Gombe shaidar girmamawa.

Kungiyar ta karrama basaraken ne saboda irin taimako da goyon baya da yake basu a duk inda yaga ana bukata. 

Wata mace daya daga cikin jiga jigan kungiyar ta kira sarki matsayin "baya goya marayu kuma UBAN KASA sannan tace gaskia godiya bazata mayarda alkhairinda sarkin keyiwa yara kanana da mata ba. 

Alh. Abubakar Shehu Abubakar tun lokacinda ya karbi sarauta jamaa ke maraba da kuma son barka ga halayensa da kulawa da alumma. 

Matashin Basaraken yazama abin koyi a dukkan jihar sakamakon saukin kai da kuma taimakon marasa galihu, hakan yasa ake kiransa da sunan UBAN KASA.