Wasu matasa sun yanke kan wani dan uwansu matashi

Matasan suna daga cikin masu garkuwa da mutane da duka addabi  wasu yankuna a Nigeria.

Shekaran jiya talata 27-11-2018 da misalin karfe 8:30pm na dare kwararrun jami'an 'yan sanda masu yaki da masu garkuwa da mutane (Police Anti-kidnapping Unit) reshen jihar Lagos, suka kama wadannan matasa 'yan uwan juna Ayodeji Obadimeji dan shekara 18 da  Saheed Obadimeji dan shekara 19 aka kamasu da guntulallen kan mutum

Bayan an kamasu aka tuhumesu sai sukace wani mutum ne mai suna Sodiq Abefe ya basu kwangilar nemo masa kan mutum akan kudi naira dubu dari biyu (N200, 000), shine sai suka nemi wani yaro suka aikeshi don ya saya musu lemon kwalba na Coca-Cola, bayan yaje ya sayo ya kawo musu sai suka kamashi suka danneshi suka yankashi suka guntule masa kai

Yaron da suka guntulewa kayi sunanshi Joseph Makinde 'dan shekara 10, an samu gangar jikinsa, sannan 'yan sanda sun matsa kaimi wajen nemo inda Sodik Abefe a inda ya boye saboda shine ya baiwa matasan kwangilar don ya fuskanci hukunci

Kwanishinan 'yan sanda na jihar Lagos ya bada umarni a mika case din ga sashen rundinar 'yan sanda kwararru a bangaren binciken kisan kai na jihar Lagos (Homicide section of the State Criminal Investigation And Intelligence Department SCIID) don cigaba da gudanar da bincike, sannan yace duk wasu masu aikata miyagun laifuka a jihar Lagos su tuba ko kuma su fice su bar Lagos don rundinar 'yan sanda ba zata kyale ba

Masha Allah Baba Buhari yayi karin albashi ga 'yan sanda dole mu ga canji.
Wannan abinda matasa suka aikata ya kamata ya zama darasi, shine makasudin da ya sa na sanar daku abinda ya faru, Matasa a kiyaye, kar neman kudi ya kaiku ga aikata miyagun laifuka wanda zaisa ku kare rayuwarku a gidan yari.