Tsohon shugaban Amurka George Bush ya rasu


Tsohon shugaban da aka fi sani da George Bush Senior ya mutu ne ranar Juma'a da yamma kamar yadda wani kakakin iyalin gidansa ya bayyana.

Shi ne shugaban Amurka na 41 tsakanin shekarar 1989 da 1993 bayan ya shafe shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa Ronald Reagan.

Amma duk kasancewa farin jininsa ya kai kashi 90 cikin 100, an tuhume shi da rashin kulawa da harkokin cikin gida, inda Bill Clinton ya kayar da shi a zaben 1992.

George Herbert Walker Bush ya fara shiga harakokin siyasa a 1964 bayan ya fara kasuwanci na man fetur inda ya zama miloniya yana da shekara 40.

Matukin jirgin sama ne a lokacin yakin duniya na biyu, amma Japan ce ta harbo jirginsa a 1944 yayin da yake kokarin kai harin bama-bamai ta sama.
Ya fito ne daga gidan masu hannu da shuni kuma 'yan siyasa a Amurka. Mahaifinsa tsohon sanatan Amurka ne.

Bush ya taba zama shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka CIA.
A 1980 ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican amma ya sha kaye a hannun Ronald Reagan, amma kuma aka ba shi mukamin mataimakin shugaban kasa.

Shi ne mataimakin shugaban kasa na farko tun 1936 da aka zaba a matsayin shugaban kasa a Amurka.

A 1988 ya sake tsayawa takarar shugaban kasa kuma ya samu nasara.
Bush ne ya jagoranci yaki wanda ya tursasawa Saddam Hussein fice wa daga Kuwait.
Bayan ya bar sojan ruwa a 1945, Bush ya auri Barbara Pierce lokacin tana shekara 18.

Ya mutu ya bar 'ya'ya biyar, da jikoki 17 da kuma tattaba kunne guda takwas.

Source: BBC HAUSA