Tsoho mai shekara 70 ya auri 'Yar shekara 15

Am daura auren ne bisa yarda da kuma soyayya tsakanin dattijon da kuma yarinyar. 

Majiya ta shaida lamarin ya faru ne jihar Niger inda dattijon mai suna Alhaji Yukubu Chanji ya aure karamar yarinyar mai shekara 15 kuma cikin soyayya har taron taya murna akayi domin farinciki. 

Hotun ma'auratan yayita yawo a kafafen sadarwa inda jama'a daga sassa daban daban na Nigeria ke tofa albarkacin bakunansu saboda zuwan abin kamar da mamaki a wannan zamani. 

Saidai masu sharhi kan Auren sunyita rubuce rubuce inda sume bayyana raayoyinsu. Wasu suna ganin hakan matsayin wata takurawa ga rayuwar karamar yarinyar, Saidai wasu kuma suna ganin hakan daidai ne tunda ba yau aka fara ba kuma abu ne ma dayake halal a musulunce kuma an gaji hakan tun iyaye da kakanni.