An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan December, 1942.
Cikaken bafulatani dan Nigeria ne, sunan mahaifinsa Hardo Adamu kuma an haifeshi ne a garin Daura dake jihar Katsina.
Buhari ya fara aikin soja ne yanada shekara 19 wato a shekarar 1962.
Ya samu nasarori dayawa a yaki daya jagoranta a rundunonij soja hakan yasa yagita samun karin girma cikin kankanin lokaci.
Buhari ya rike manyan mukamai na soja kafin yazama Gomna na soja kana daga bisani akayi juyin mulki yazama shugaban kasa na mulkin soja.
Muhammadu buhari ya shiga harkokin siyasa kuma ya fara takarar shugabancin kasarnan a zaben 1999 inda suka fafata da Chief Olusegun Obasanjo amma bai samu nasara ba Obasanjo ya zama shugaban farko na democracy a Nigeria.
Buhari ya sake neman takara a shekarar 2003, 2007, 2011 har zuwa 2015 da yayi nasarar kayarda Goodluck Jonathan ya kuna karbi ragamar mulki.
Rayuwar Buhari tazama abin koyi ga mutane dayawa saboda tsantseni da yakedashi tun yana aikin soja.
Shi mutum ne da yakeda farinjinin talakawa fiyeda kowane dan siyasa a Nigeria.
Yanada ra'ayin kawo sauyi a kasa musamman bangaren yaki da cin hanci.
Yanada kawar dakai a kan dukiyar kasa kuma baya son ana almubazzaranci da kudin kasa.
Yanada iyalai da kuma jikoki dayawa a gidajen 'ya'yansa mata da sukai aure.
Sunan matarsa
Aisha Buhari.
Sunaye 'ya'yansa:
Zulaihat (deceased)
Fatima
Musa (deceased)
Hadiza
Safinatu
Aisha
Halima
Yusuf
Zarah
Amina
A halin yanzu Shine shugaban kasa mai cikaken iko kuma ya sake tsayawa takara domin samun nasara a zaben da zasu fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar 2019

