Ni Buhari ne na gaskia bana bogi ba -Inji Shugaba buhari

Shugaban ya maida martanin ne yayin wata ganawa da manema labarai a kasar Poland. 

Kusan watanni 2 kenan da fara takaddama kan labarinda ke yawo a wasu jaridu ana zargin cewa shugaban na bogi ne ba ainihin wanda aka zaba a 2015 ba. 

Saidai shugaban ya maida martani domin kawo karshen takaddamar.

Buhari ya ce: "Da yawan mutane suna zargin cewa wai na mutu anyi madadina da wani. Amma a zahiri ba gaskia bane, Zanyi biki murnar zagoyawar cikon shekara 76 a duniya nan bada jimawa ba. 

Da yawan masu yada labarin cewa shugaban na bogi ne suna kafa dalili ne da wasu hotuna ko dabi'u na shugaban musamman idan aka kwatanta yadda yake lokacin rashin lafiya da lokacinda yake lafiya kalau. Sannan kuma masu yada labarin suna kafa hujjar cewa lokacinda shugaban yayi rashin lafiya ya mutu kamar yadda suke zargi an dauko wanine ya maye gurbinsa. 

Zuwa yanzu ta iya yiwuwa a rufe shafin zargin saboda yadda shugaban ya maida martani mai ma'ana ga wadanda suke tunanin haka.