Matar shuganan kasar ta bayyana hakan ne a wajen wani babban taro da aka gudanar domin tallafawa mata.
Aisha Buhari tace "Hakika akwai mutane uku da suke juya shugaban kasar Nigeria wadannan mutane kuma babu wani shirin cigaba da suke kawowa shugaban.
"Mutane milyan 15 ne suka zabi mijina a shekarar 2015 amma sai gashi anbar mutane uku suna juyashi hakan ba daidai bane.
Irin wadannan zarge zarge da kuma kalamai ba yau suka fara fitowa daga bakin uwar gidan shugaban ba. Tun bayan samun nasarar mai gidan nata Shugaba Muhammadu Buhari.
A baya ma mutane sunyita irin wadannan zarge zarge saidai har yanzu baaji wani martani daga bangaren shugaban kasar ba.
Mutane dayawa sun tofa albarkacin bakunansu saboda yadda matar shugaban kasar take yawan kalamai kan gomnatin ta Buhari. Saidai mutane dayawa na ganin kamar wani kafar ungulu take yiwa gomnatin saidai kuma wasu dayawa suna kallom abin a matsayin wani yunkuri na tallafawa wajen nuna kura kurai da yakama gomnatin tayi gyara.

