Masoyi ya kashe budurwarsa a jihar Rivers

Yan sanda sun cafke wani matashi da laifin kashe budurwarsa a karamar hukumar  Opio local Government dake jihar Rivers.

An gano gawar mamaciyar ne a dakin saurayinta bayan kwashe tsawon kwanaki ana bincike kana daga bisani aka samu gawar a dakin.

Mutumin wanda aka fi sani da j-boyya kashe budurwar tasa ne sakamakon rashin jituwa data afku tsakaninsu lokacinda ya gano tana soyayya da wani saurayi daban.

Wani dan uwan mamaciyar ya shaidawa manema labarai cewa " a ranar 2 ga watan December ne muka nemi yar uwata muka rasa kana muka fara yawon neman inda zamu sameta kuma gar wurin saurayin nata munzo amma yace shi baisan ina ta shiga ba dole muka hakura muka garzaya zuwa wurin 'yan sanda domin cigaba da bincike.

" A gaskia wannan abin bakin ciki ne dukda sun kasance masoya ne suka samu sabani, Wannan ba abin kyalewa bane bazamu taba bari a rufe wannan maganar ba dole sai koti ta bi mana kadun kisan 'yar uwarmu da akayi.

Daruruwan mutane ne suka kewaye unguwarda da lamarin ya faru domin ganewa idonsu abinda ya faru. Yayinda yan jaridu suke tuntubar shaidun gani da idon sun bayyana kiraye kirayensu ga hukuma don tabbatarda adalcj kan wannan aika aika da aka yiwa matashiyar.