Masarautar Kano ta karrama Naziru M Ahmad (Sarkin Waka)

Sanarwar bada sarautar ta fito ne daga bakin shugaban ma'aikata na masautar ta Kano. 

An baiwa mawakin ne sarauta mai taken Sarkin wakar sarkin Kano. 

Masarauntar Kanon ta baiwa mawakin wannan babbar sarauta ne saboda saboda irin kokarinsa wajen yiwa mai martaba sarkin Kano dad'ad'an wakoki daban daban tun sanda aka bashi Dan majen Kano lokacinda yake aikin Gomnan bankin Nigeria CBN. 

Wakar Naziru ce ta fara bazuwa a gari kuma tafi kowace waka ficelokacinda aka nadin sarautar Sunusi Lamdio Sunusi matsayin Sarkin Kano. 

Za'a yi bikin nadin sarautar a fadar mai martaba sarkin Kano A ranar 27 ga watan December 2018.