LABARAI: Anyi garkuwa da 'yan agajin IZALA

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wata tawagar 'yan agaji da suke kan hanyar dawowa daga Atisayen kasa da aka gudanar a jihar jigawa. 

Lamarin ya faru ne bayan kammala atisayen wanda ya tara dubban 'yan agaji da suka hada dukkan jihohin arewacin Nigeria.

Anyi garkuwa da jami'an 'yan agajin ne yayinda suke kan hanyar komawa gida jihar sokoto.

Zuwa yanzu ba'aji wata sanarwa ko labari na cewa an gano su ba saidai mutane nata addu'o'i garesu. 
Garkuwa da mutane yana neman zama ruwan dare kuma babbar barazana ga alummar Nigeria musamman arewaci da basu jima da fita daga fargabar rikicin BOKO HARAM ba.