Kotu ta daure Farfesa da ya nemi lalata da dalibarsa

Babbar kotun dake zaune a birinin Ile-ife dake jihar Osun ta yankewa farfesan hukunci ne bayan kammala bincike da gano gaskiar al'amari daya faru tsakaninsa da dalibar tasa. 

A watannin da suka wuce ne aka kai karar farfesan mai suna RICHARD AKIDELE bisa zargin neman lalata da wata dalibarsa MONICA OSAGIE dake a matakin 400level domin bata nasara a jarabawarta.

A Ranar litinin 17 ga watan dec 2018 kotun ta zauna da dukkan lauyoyin bangarorin biyu kana daga bisani ta yankewa farfesan hukuncin zama gidan kaso har tsawon shekara 3.

Kafin yanke hukuncin kotun ta shaida cewa aikata hakan laifi ne a dokar kasa kuma cin zarafi ne ga dalibai da kuma neman batawa makarantun gaba da sakandare suna. 

Shima wanda ake zargi Farfesan ya amsa zarginda ake masa inda ya bayyanawa kotun cewa shi mai laifi ne dukda cewa a baya yayi ikirarin bai aikata abinda ake zarginsa ba. 

Neman lalata da dalibai don basu nasar a sakamakon jarabawa a jami'o'in Nigeria yazama ruwan dare musamman a kudancin kasar.