Hukumar HISBA ta fasa mota guda ta giya a Kano

Hukuma  Hisba mai kula da hakkokin da suka ci karo da addinin musulunci da rayuwar musulmai tayi kamen motar giyar ne lokacinda aka daukota daga jihohin kudanci zuwa cikin garin Kano. 

Shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shine ya jagoranci fasa kwalaben giyar wadanda adadinsu zai iya kai roka 2.

Hukumar HISBA ba tun yau tafara irin wannan aiki ba tababa, tun sanda aka kafa hukunar a zamanin tshohon gomna Mal. Ibrahim Shekarau. 
Saidai wasu inyamurai da kabilu mazauna garin kano sun nuna rashina jin dadinsu kan lamarin ganin cewa mafi yawa ba wai musulmai ne ke mafani da giyar idan an shigar daita Kano.