Jam'iyyar PDP ta fara gudanarda yakin neman zabe a jihar Sokoto.

Dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar tareda tawagarsa, Daraktan neman zabensa Sen. Bukola Saraki, Shugaban Jam'iyyar PDP Secondus da kuma Gomnan jihar Sokoto Alh. Aminu Waziri Tambuwal.
Dubban mutane ne suka fito domin tarbar dan takarar kamar yadda ya daura hotunan taron a shafinsa na sadarwa.
Har yanzu Jam'iyyar mai mulki bata fara nata yawon neman zaben ba.