Diyar Donal Trump zata auri dan wani shahararen mai kudi a Nigeria

Michel tareda Tiffany 

Yarinyar wacce diyace ga shugaban Amurka Donal Trump ta bayyana jin dadinta gameda alaka da saurayin nata wanda tuni ya gana da mafi yawan 'yan uwanta domin tabbatarda baiko tsakaninsu.

Yaron mai suna Michael ya kasance d'a ne ga wani babban gidan masu arzikin bilyoyin dalar Amurka. a jihar Lagos. 

Michel yaro ne mai hazaka da kuma kaifin basira, wanda da ne ga wani mai kudi a Nigeria wato Boulus.

Masoyan Michael da Tiffany sun jima tare kuma suna rayuwa ne mai matukar soyayya da shakuwa aciki wacce takai ga samun babban daidaito tsakaninsu har suke shirin kulla yarjejeniyar aure.

Saidai kuma abinda ke daukar hankali kan batun yarjejeniyar auren shine yadda mahaifin yarinyar wato Donal Trump yakeda mummunar akida kan yan africa wanda hakan ne yasa yake ganin nahiyar wata cima baya a Duniya.

Shin ko shugaban na Amurka zai sake kalaman batanci ga africa idan diyar tasa ta auri saurayin nata Michael? Wannan shine abinda duniya take jiran gani har zuwa lokacin auren masoyan.