Bazamu sake sauraron zama da gomnati ba - Inji ASUU

Kungiyar malaman jami'o'i ta bayyana cewa bazata sake jiran wani zama da gomnati ba sakamakon rashin daidaito da suka samu a dukkan zaman da sukayi da gomnatin.
Zaman sulhu da sukayi da ita.

Shugaban kungiya yace sunyi zama sau 6 da jami'an gomnati amma dukkan zaman basu samu daidaito ko daya da gomnatin ba.

Saidai bangaren gomnati basu maida martani kan kalaman kungiyar ba amma idan baku manta ba kwanakin baya gomnati ta gargadi kungiyar kan cewa za'a dakatarda biyansu albashi matukar suka ci gaba da yajin aikin.

Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki tun ranar 4 ga watan November bayan sun bayyana maradunsu da kuma rashin cika alkawari da gomnatoci ke musu.

Yanzu haka dalibai na cigaba da zama a garuruwansu wasu kuma tuni suka bazama neman aikinyi kafin dawowar ASUU daga dogon yajin aikin data shiga.