Babu wanda yake juya ni a Nigeria -Martanin Shugaba buhari

Shugaban kasar Nigeria Muhammadu buhari ya maida martani kan zarge zarge da wasu 'yan Nigeria sukayi kan ana juya akalarshi. 

Shugaban yace "Babu wanda yake juya ni kuma babu wanda zai samu damar haka domin ni ba yaro bane nasan shawararda zata amfane ni nasan wacce zata cutar dani. 

Yayinda Dan jaridar VOA HAUSA ya tambayi shugaban kan cewa cikin masu zargin haka harda matarsa,  sai Buhari ya kara da cewa " Na fada ai bin tsarin demokradiyata yasa kowa ke fadar albarkacin bakinsa amma idan akwai wanda yake tunanin lallai juya ni ake to na kalubalanceshi ya kawo abu guda da sanya ni akayi ba ni nai ba. 

Ko a kwanakin baya uwargidan shugaban AISHA BUHARI tayi wasu zafafan kalamai akan gomnatin mijin nata inda ta bayyanawa duniya cewa wasu mutane da basu wuce 3 ba suna juya shi.

Zarge zarge sun jima da yawo a tsakanin 'yan Nigeria dayawa kan batun wasu mutane na juya shugaban sai yadda suka bukata akeyi.