Babu sauran kofar sata ga barayin dukiyar Nigeria -Ibrahim Magu

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa IBRAHIM MAGU yayi wannan bayani ne yayin amsa tambayoyin 'yan jaridu a a wata gayyatar taro daya halarta na cibiyar ilimi ta CIN.

Ibrahim Magu yace" Yanzu babu sauran wata dama ko sararin sata ga barayin kasarnan saboda mun shirya tsaf domin yaki da duk wata barna ko wawurar kudaden alumma.

"Bai kamata mu bar wannan hukuma kadai ce zatai yaki da cin hanci ba, Wannan aiki ne na duk wani dan Nigeria mai kaunar cigaba da kuma kishin kasar Nigeria.

Ibrahim Magu ya kuma yi kira ga 'yan Nigeria Masu katunan zabe, Yana mai kira da babbar murya da su zabi mutane masu gaskia da adalci, Kada su zabi wadanda zasu wawure dukiyarsu ba tareda sun amfana musu komai ba.