Atiku da Osinbajo sun gana da juna a jihar Bauchi

Karanta yadda haduwarsu ta kasance sa inda suka hadu.

Jagororin biyu sun hadu ne yayin halartar babban taron daura auren diyar tsohon Gomnan Bauchi Alh. Adamu Mu'azu.

Atiku da Osibanjo sun gaisa cikin girmamawa da kuma fara'a a fuskar kowannensu kai kace babu adawar siyasa tsakaninsu.

Bayan sun gaisa sunyi tattaunawa gajeruwa kafinnan kowa ya zauna a wurinda aka tanadar masa.

Yadda haduwarsu da girmama juna da sukyi yasa mutanen dake wurin suka dau farinciki da ganin abin burgewa sukayi .

To dama dai masanan siyasa sun ce ba'a makiyi ko masoyi na dindin din a siyasa.

Wannan ya ragewa talakawa suma suyi taka tsantsan wajen siyasa kuma su girmana raayin kowa babu tsangwama don mutum yayi nasa raayin. Babu fada babu bakar magana haduwa a rumfar zabe kowa ya zabi gwaninsa shine mafita kuma hanyar samun siyasa mai kyau da tsafta a Nigeria.