Atiku Abubakar ya ziyarci Sheikh Dahiru Bauchi

Dan takarar ya ziyarci Shahararen malamin addinin ne a gidansa da ke Bauchi. 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gaisa da dan takarar na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar bayan haka yayi masa adduada kuma fatan alkhairi.

Haduwar ta kasance ne bayan daura auren diyar tsohon Gomnan jihar Bauchi Alh. Adamu Mu'azu.

Mutane dadama sunyita tofa albarkacin bakunansu akan ziyarar saidai magoya bayan Atiku sun maida martani da cewa ziyara ce kawai ta girmamawa ga babban malamin.