Anyi karar shugaba Buhari a kotu saboda badakalar Ganduje

Wata kungiya mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ta maka shugaban Nigeria Muhammadu Buhari a kotu sakamakon rashin bada umarni a bincika badakalar kudade da ake zargin ganduje.

Kungiyar mai suna SIRAF ta kai karar shugaban ne a wata babbar kotu dake zaune a jihar Lagos.

Jagororin kungiyar sunce shugaban ya nade hannunsa ne sabida wani kuduri na siyasa wanda bai kamata ya shigo cikin harkar yaki da cin hanci ba.

Idan masu karatu basu manta ba a kwanakin baya wata kotu ta dakatarda majalisar da kuma kwamiti da yake bincike don gano gaskiar lamarin badakadar da ake zargin gomnan Kano Abdullahi Ganduje.

Saidai kuma haryanzu baaji wani martani kan kai karar shugaban kasar ba saidai masu sharhi da mabiya shugaban Muhammadu Buhari suna ganin wani shiri ne kungiyar sukayi don shafawa shugaban kashin kaji.