An kama mutumin ne bayan ya rufe matarsa awani daki da babu haske kuma ba'ajin hayaniyar mutane.
Rahotanni sun bayyana sunan mutumin Mariuez Sz cikaken baturen England ne.
Mr. Sz ya killace matar tasa ne a inda babu mai iya gane ya boyeta, sannan yana bata abinci kamar yadda ake baiwa dabbobi saita durkusa take cin abincin. Yayita yi mata fyade a aduk sanda ya bukata kana daga bisani ya rika karbar kudi a hannun abokai da wasu 'yan uwansa guda biyu suna fyade da ita.
Sauran masu laifin sunyi fyaden ne a farashin kudi da bai wuce kamanin 2,000 a kudin Nigeria.
Bayan asiri ya tunu ne aka kama Mr. Sz mijin matar sannan aka gudanarda shi a gaban kotu inda ta yanke masa hukuncin zama a gidan yari tsawon shekara 25.
Wani lauya mai kare hakkin bil'adama ya bayyana cewa abinda mutumin ya aikata laifi ne babba domin ya take hakkinta na dan adamtaka sannan ya muzguna mata da zubard kima wajen bada hayarta ga wasu maza.

