Ana tuhumar mariyatu ne da laifin damfarar mutane a matsayin 'yar uwa ko wakiliya ce ga matar shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari.
Matar mai suna Mariyatu ta jima tana amfani da sunan Aisha Buhari inda take zuwa wuraren yan siyasa da kuma manyan maaikatan gomnati tana karbar kudade. Sannan kuma sunayenta na karya sunkai guda biyu wadanda duk damfarar take da su.
Kafin akama Mariyatu, hukumar DSS tayita zarya wajen matar shugaban kasa Aisha Buhari domin tambayoyi da tabbatarda basu da alaka da yarinyar.
Saidai kuma Uwar gidan shugaban kasa Aisha ta bayyana rashin jindadinta ga wannan badakala da kayi da sunanta kuma ta nesanta kanta daga wannan mummunan aiki.
Aisha Buhari tace " Ni bantaba ganin mriyatu ba arayuwata gaba daya kuma bamuda alaka ta kusa ko ta nesa da ita. Sannan kuma ban taba hada alaka da ta aiki ko huldar kasuwanci da ita ba, Nayi mamakin yadda harta iya kama sunana da sanin wasu bayanai nawa wadanda take amfani dasu wajen damfara ga mutane.
Hukumar DSS tace zata cigaba da rike Mariyatu har sai an gama bincike gameda badakalar.
Idan baku manta ba a kwanakin baya ma an kama wani jamii mai kula da tsaron Aisha Buhari wanda shima dai akan irin wannan laifin haryanzu ake tsare dashi.

