Wani dan takarar fidda gwani daya fadi a Jam'iyyar PDP ya baiwa Jam'iyyar awanni 24 domin ta rushe zaben fidda gwani da tayi a jihar rivers wanda Atiku Abubakar ya lashe.
Dan takarar mai suna Mr. Stanley Osifu ya fadi haka ne a wata ganawa da sukayi da manema labarai a jihar Lagos.
Mr. Osifu yace Jam'iyyar batai masa adalci ba a yayin gudanarda zaben kamar yadda ya shaidawa yan jaridu.
Yace" Ni cikakken dan Jam'iyyar PDP kuma na sayi fom fin takara da suka sayar kan naira milyan 10 amma abinda ya hasala ni shine basu bani cikakiyar dama kamar yadda suka baiwa sauran 'yan takara ba.
" Saboda haka ina shawartar Jam'iyyar da tayi gagawar sake sabon zaben fidda gwani domin ni ban aminta da abinda tayi a zabukan da aka gudanar a baya ba.
Saidai magoya bayan Atiku sunyita maida martani kan kalaman Mr. Osifu inda dayawansu ke ganin watakila kudinda ya sayi fom din yake bukata Jam'iyyar ta mayar masa.

