Tsohuwar jaruma Rahama Hassan ta baiwa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2019.
Bayanin Hajiya Rahama ta wallafa ne a shafinta domin kira ga masu zabe.
Ga sakon nata kamar haka:
Ina muku fatan Alkhairi, Sannan inaso na bamu Shawari kasantuwar lokacin zabe ya gabatoWallahi babban abinda ya kamata muyi shine Addu'a da niyyar Allah mana zabi Nagari
Domin Wannan Zage zage da bata juna da cin zarafin juna akan yan siyasa bazai taba zabo mana Shuwagabanni nagari ba.
Sannan Matasa wallahi kuji tsoron Allah kudaina fifita Bukatun kanku akan na Al'ummar ku, in ba haka ba kuma cigaba sai dai mugani a wata kasa
Muna rokon Allah wanda yafi sanin irin halin da kasar take ciki da ya mana rahama ya bamu Shuwagabinni nagari

