Yadda tagwayen zamfara suka samu nasarar dawowa gida

An samu nasarar dawowar hassana da hussaina wadanda akayi garkuwa dasu a jihar zamfara.

Anyi garkuwa dasu ne tun kusan wata daya suna hannun wasu mutane da baa san ko suwaye kuma a ina suke ba.

Jaridar DailyNigerian ta zanta da tagwayen a yau asabar kuma sun shaidawa manema labarai cewa sun dawo gida lafiya ba tareda cutarwa ba.

Labarin tagwayen ya shahara cikin kwanakinnan tun bayan sacesu wanda rashin nuna damuwar gomnati akan lamarin ya tilastawa 'yan uwansu shelanta labarin kana daga bisani suka nemi taimakon kudi kimain naira milyan 15 domin baiwa masu garkuwa da tagwayen kamar yadda suka bukata daga makusantan 'yan biyun wadanda talakawa ne ba masu hannu da shuni ba.

Wani senata a jihar zamfara kabiru marafa ya bada gudunmawar milyan 6 sannan kuma sai jama'a da suka harhada taimakon kudaden har milyan 9 ya cika milyan 15.

Tun bayan sace yaran har zuwa dawowarsu gomnati batace uffan akan lamarin ba hakan yasa jama'a sukaita suka ga yanayin halin ko in kula da gomnatin jihar zamfara da kuma tarayya sukayi akan tagwayen.