A ranar juma 19 ga watan november, mayakan boko haram suka hallaka jami'an sojojin Nigeria kimanin guda 70 a wata fafatawa da sukayi.
Jaridar Premiums Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani kauye mai suna Metele wanda ke karkashin karamar hukumar Guzama a jihar Borno.
Daya daga cikin sojoji da suka tsira da ransu ya shaidawa manema labarai cewa 'Harin bai wuce tsawon mintuna 45 ba, kuma rashin nasarar sojojin ta faru ne sakamakon rashin ingantattun makamai wanda hakan ya haifarda kashe sojojin da kuma kwashe motocin yakinsu, bindigoginsu da alburusai masu yawa.
Dukda cewa a shekarar 2015 shugaba Buhari ya bayyana cewa Boko Haram ta mutu saidai kuma bayan maganar tasa ya zuwa yanzu adadi mai yawa na sojoji sun hallaka a fagen yaki da BOKO haram.
Ko a watan October, and wata fafatawa da kimanin sojoji 157 suka jikkata inda guda 18 suka rasa ransu sannan kuma adadi mai yawa sun bata ba'a san inda suke ba.
Dayawan jami'an sojoji sun shiga mawuyacin hali sakamakon rashin 'yan uwansu.
Masu sharhi a kafafen yada labarai da na sadarwa suna kan bayyana ra'ayoyinsu akan mutuwar sojojin yayinda wasu ke miki taaziyya ga iyalan mamatan wasu kuma suna sukar gomnati ne bisa rashin fadin gaskia da kuma damuwa da ire iren hare haren kungiyar BOKO haram akan sojoji.

