TSAKANIN BUHARI DA ATIKU, WA ZAI LASHE ZABE?

* Nazarin Hasashe: Yadda sakamakon zaben 2019 zai kasance.

Daga: Mohammed Ibrahim

Yau Lahadi 18 ga watan Nuwamba, 2018. Yau ce ranar farko da Hukumar INEC ta ce a fara yaqin neman zabe. Bisa ga haka, maimakon wannan shafi ya yaba wa wani dan takara, sai ya ga gara ya fara da nazarin hasashe a kan Buhari da Atiku a matsayinsu na manyan 'yan takaran shugaban qasa wadanda ake da tabbacin cewa dayansu ne zai yi nasara. Shin a cikin su wanne ne zai yi nasarar lashe zabe mai zuwa?

Hangen haka mai sauqi ne idan aka yi la'akari da dalilai da buqatun masu zaben bisa ga awon rabe-rabensu kamar haka:

1. Shiyyoyi

A Nijeriya akwai shiyyoyi shida. Uku a Arewa, uku a Kudu. Su ne shiyyar Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta tsakiya. Sai kuma Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu ta Kudu.

An samu daidaito a kan cewa shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu ta Kudu ba za su zabi Buhari ba. Saboda PDP (jam'iyyar Atiku) ce jam'iyyarsu, da dadi ko ba dadi.

A Kudu maso Yamma kuwa, jiga-jigan siyasar ta uku ne. Su ne qungiyar Afenifere da Bola Tinubu da Obasanjo. A cikin su, Afenifere da Obasanjo, zuwa yanzu, sun nuna goyon bayansu ga Atiku. Bola Tinubu ne kadai aka bari da mara wa Buhari baya, ba tare da irin karsashin da ya nuna a zaben shekarar 2015 ba.

A Arewa maso Yamma, alamu na nuna za a raba gari ne. Saboda akasarin jiga-jigan 'yan siyasar shiyyar, a yanzu suna tare da Atiku ne. Ga wasu daga cikinsu. Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a Kano, Alhaji Sule Lamido a Jigawa, Alhaji Ahmed Makarfi a Kaduna, Alhaji Dalhatu Bafarawa a Sokoto, Alhaji Shehu Shema, a Katsina, da Matawallen Maradun a Zamfara. Kowanne daga cikin wadannan yana da tawagar mutane da ke binsa duk inda ya sa qafa. Kazalika su ma a cikin talakawan, zuwa yanzu, an samu kaso mai dama a cikinsu da ke shirin zaben Atiku. Hakan ba ya rasa nasaba da rashin aminta da salon mulkin Buhari.

Haka abin yake a Arewa maso Gabas, nan ma za a raba gari ne. Masu son mulki ya dawo shiyyarsu, za su zabi Atiku, masu ganin gwamnati mai ci ta daqile barazanar Boko Haram a shiyyar, za su zabi Buhari.

Amma ba haka lamarin yake a shiyyar Arewa ta tsakiya ba. Farfagandar rikicin makiyaya, da tasirin siyasar Bukola Saraki za su taka rawa ainun wurin hana jama'a zaben Buhari. Qari da cewa, mutanen shiyyar, ba sa ganin Buhari da siffar nan ta tsarki irin wacce ake kallonsa da ita a qwaryar Arewa. Wannan zai sa su fi mizanta Buhari da abin da ya aikata.

2. Addinai

Dukkan Kiristocin Nijeriya, ko kuma a ce kashi 90 nasu, za su zabi Atiku ne. Saboda sun fi gamsuwa da salon siyasarsa ta rashin nuna karkata ga addininsa a zantukansa da sauran harkokinsa.

A cikin Musulmi kuwa, kusan kowace qungiya tana da nata kason da ke son Buhari da kason da ke son Atiku. Misali, Sufaye, galibinsu ba za su zabi Buhari ba, saboda ganin ya nuna karkata ga Wahabiyawa. Su kuma Wahabiyawa galibinsu za su zabi Buhari ne, saboda ganin ya yi mu su maganin 'yan Shi'a. Su ma kuma 'yan Shi'a, galibinsu ba za su zabi Buhari ne saboda ganin ya karkashe mu su 'yan uwa.

3. Matsayai

Akasarin masu kudi da masu harkokin kamfanoni ko 'yan buge-buge za su zabi Atiku, hususan saboda hangen cewa, da salon mulki irin nasa ne harkokinsu za su dawo kamar yadda suke ko kuma ma su fi yadda suke a baya.

A cikin tantagaryar talakawa da ma'aikatan gwamnati masu qaramin matsayi da ke Arewa za a fi samun kaso mai yawa na wadanda za su zabi Buhari. Saboda a wurinsu, salon mulkin Buhari ya dace matuqa.

Idan har ba wasu lamurra suka taso ba, a yadda ake din nan, in har aka tafi a haka, to sakamakon ke nan a hasashen wannan shafi. Saura da me? Shafin ya bar wa mai karatu damar buga lissafi a kan hasashen, don ganin wanda zai lashe zabe a tsakanin mutum biyun nan.

Muhammad Bin Ibrahim
18/11/2018