Karanta cikaken dalilinda yasa Atiku Abubakar kafin ka yanke masa hukunci.
Jaridar Punch ta 19 ga Oktoba 2018 ta ce:
"Domin a bunqasa bangarorin mai da gas, Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai sayar da wani bangare na Kamfanin Man Fetur na qasa (NNPC) don tabbatar da an samu masu kulawa cikin gaskiya da riqon amana."
Abin da jaridar ta ce shi ne, wani bangare na NNPC ba duka ba. Amma abin mamaki, maimakon a tsaya a fahimci hikimar Atiku ta son hakan, sai aka fara baqanta shi da son sayar da qaddarar qasa.
Shi da kansa ya fayyace abin da yake nufi a Kundin Manufofinsa. Ga abin da ya ce:
"We shall privatise all four outstanding government-owned refineries to competent off-takers with mandates to produce agreed levels of refined output."
Ma'ana: "Za mu sayar da matatun mai hudu na gwamnati ga 'yan kasuwan da suka cancanta bisa sharadin za su riqa tace man da za a buqata."
Ke nan ashe ba sayar da kamfanin NNPC zai yi kacokan ba, a'a, wani bangare ne, wato matatun nan na mai guda hudu.
Mene ne NNPC?
NNPC taqaitacciyar kalma ce daga "Nigerian National Petroleum Corporation," wato Kamfanin Man Fetur na Qasa. Kamfani ne wanda gwamnatin tarayya ke gudanar da harkokin man fetur na qasa da shi. An kafa shi a 1977, kimanin shekara 41 da suka gabata.
Ayyukansa sun hada da nemo muhallin da mai yake, haqo shi, da fitar da shi. Cikin abubuwan da yake fitarwa kuma akwai man fetur, gas, da ababen da ake sana'anta su daga man fetur, irin su kalanzir, gasolin, man injina, da makamantansu, da kuma kemikals din da ake tacewa daga man fetur (petrochemicals).
NNPC yana da rassa kamar haka:
DUKE OIL, Hyson, IDSL, KRPC, NETCO, NGC, NPDC, NAPIMS, NIPEX, PHRC, PPMC, WRPC, NNPC RETAIL da
NNPC Pensions Limited.
A cikin rassan kamfanonin nan, reshen PPMC ne ke da alhakin karbar danyen mai (crude oil) daga reshen NAPIMS, sai ya aika wa matatun man fetur na gida don su tace su sayar wa 'yan Nijeriya. Idan kuma matatun man suka kasa tace isasshen man da ake buqata, sai a sayo mai daga waje kamar yadda ake yi yanzu.
Wadannan matatun man fetur din su ne Atiku ya ce zai sayar idan Allah ya sa ya zama shugaban qasa.
To a kan me zai sayar?
Ya ce saboda a samu wadanda za su riqe su tsakani da Allah ba tare da algus ba. Kuma ya ce saboda ya qara samun damar yin amfani da hakan wurin samar da aikin yi mai gwabi ga kimanin mutum miliyan guda a bangaren NNPC kawai zuwa shekara ta 2025.
Ba sai an fada ba, kowa dai ya san tulin matsalolin da ke tattare da matatun man fetur dinmu na gida. Ba sa aiki. Waje ake zuwa a sayo man fetur da sauran ababen da ake fitarwa daga gare shi. Wannan abin takaici ne a qasar da ke da arziqin mai, a ce wai wanda 'yan qasar za su yi amfani da shi sai an je waje an sayo. Dole mai ya yi tsada. Hakan kuma yana shafar tattalin arziqin qasa ta dukkan fuskoki. Saboda komai yana da nasaba da sufuri. Don haka gwargwadon yadda tsadar mai yake, haka farashin komai zai kasance.
Fata na qarshe ta qare ne da Shugaba Muhammadu Buhari. A lokacin da ya zo, an dauka za a shayo kan matsalolin nan na man fetur, kuma matatunmu na mai za su koma ga aiki gadan-gadan, saboda zaton da aka yi masa. Ashe-ashe dai, duk kanwar ja ce. Shi ma ya gaza yin komai a kai, duk kuwa da cewa ya ba wa kansa matsayin babban ministan mai din.
Tun daga hawan mulkinsa zuwa yau, jaridun Nijeriya sun shaida rikice-rikicen algus, almundahana da sauran ta'asosi iri-iri a bangaren NNPC din nan. Mai son tabbatarwa ya binciki wadannan kafafe:
A ranar 6 ga Oktoba, 2017, Blueprint ta buga rahoton zargin kwarafshan a tsakanin shugabannin NNPC biyu: Qaramin Minista Ibe Kachikwu da Babban Manajin Darakta na kamfanin man, Maikanti Baru.
A ranar 24 ga Janairu, 2018, The Nation ta wallafa fallasar da Sanata Dino Melaye ya yi kan yadda ake cuwa-cuwa a kamfanin na NNPC.
Rahoton binciken KPMG wanda jaridun Nijeriya suka ruwaito a ranakun 17-18 ga Mayu, 2018, ya kira NNPC da "Rumbun Almundahana."
Wannan yana nuna yadda harkar kwarafshan ta daskare a zukata, ba za a bari 'yan Nijeriya su amfana da NNPC ba. A kan haka ne Atiku ya tsara cewa, idan har Allah ya ba shi shugabancin qasar nan, zai sayar da matatun man don kowa ya huta. Hikimarsa ita ce, idan matatun man suka zama mallakin 'yan Kasuwa, za su sa ido sosai a kai, ba za su bari a yi abubuwan da ake yi yanzu na kwarafshan ba. Hakan kuma zai amfanar da talaka ne, domin duk yadda wadanda suka sayi matatun man suka tsauwala farashi, ba zai kai tsadar sayo shi wanda 'yan kasuwan ke yi daga waje ba. Kuma tashin matatun man fetur din, ko da kuwa a hannun 'yan jari hujja ne, yana nufin samuwar ayyukan yi ga 'yan Nijeriya barkatai. Kazalika gwamnati za ta huta da biyan maqudan kudin sobsidi (tallafi), sai ta yi wata hidimar da su.

