Tshohon mataimakin shugaban kasa
Atiku Abubakar yayi karin albashi Dukkan Ma'aikatan da suke aiki a karkashin dukkan kamfanoninsa.Hakan ya biyo bayan karin albashi da kungiyar kwadago ta matsa lamba ga shugaba Muhammadu Buhari kan dole ya karawa Ma'aikatan albashi sakamakon hauhawar farashin kayayyakin masurufi da kasar ke ciki.
Saidai jamaa dayawa suna kan bayyana raayoyinsu a shafukan sada zumunta inda wasu ke ganin kamar wani sabon salon siyasa ne Atikun keyi saboda neman karin magoya baya. Wasu kuma na ganin hakan ya nuna cewa da zarar ya hau kujerar mulki zai duba yiwuwar sake karawa Ma'aikatan kudi da kuma kula da walwalarsu.

