Tsakanin Gomna Ganduje da Jaafar Jaafar

GAME DA GANDUJE, JAAFAR JAAFAR KAN YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA.

Daya daga cikin hanyoyi ko matakan da muke bi wajen bincike kan zargin cin hanci da rashawa, wanda CATBAN take aiki da shi, shine -  Lallaban mai laifi. Ta wannan hanyar, a lokacin da duniya ta addabi wanda ake zargi da kalaman batanci, mambobin mu basu yin haka, zasu kusanci wanda ake zargi tare da faranta masa rai. Hakan zai bude mana kofofi masu yawa don aiwatar da bincike. Wannan dabara tayi mana aiki a mafi yawan lokuta kuma tana kan yi mana aiki. Abu mai muhimmanci a nan shine, muna amfani da wannan tsari ne kawai akan mambobinmu da suke da kusanci da wanda ake zargi.

Lokacin da CATBAN ta samu labarin majigin Gwamna Ganduje na jihar Kano yana karban cin hanci da rashawa daga mai wallafa labarai na Daily Najeriya Jaafar Jaafar, wasu kungiyoyi karkashin hadin gwiwarmu sun yi ta rige rigen zuwa hedkwatarmu, hakazalika, wadanda suke nesa ma sun kira mu, kusan dukkansu sun nemi mu goyi bayan Jaafar Jaafar. Amma kadan daga ciki ne suka so mu goyi bayan Gwamna Ganduje.

Mun dauki majigin kuma mun yi nazari iyakar iyawarmu akanshi sannan muka cimma matsayar kawo dalilai fiye da abinda ke cikin bidiyon. Wasu daga cikin mu, sun kawo “dalilan siyasa” na bita-da-kulli akan Gwamna Ganduje. Ma'ana, wasu daga cikin mu, sun yi kwakwanton amincin Jaafar Jaafar da kuma dalilansa. Dalilin da ya kawo irin wannan mummunan zato shine Jaafar Jaafar shine mutum na farko da ya fara tsoma baki a lokacin da CATBAN ta wallafa takardar tuhumar shugaban Hukumar aikin Hajji. Har ma wasu daga cikin mambobin wata kungiya irin tamu suka yi magana akan Jaafar Jaafar, maimakon yayi duba izuwa tuhumar da aka yiwa Hukumar aiki Hajjin, sai ya roki a cire abinda IG Wala ya wallafa. A lokacin ne IG Wala ya gano yadda Jaafar ya kalubalance shi a idon duniya, wai don me zai wallafa aibu akan maigidan shi. A lokacin da IG Wala ya tambayi Jaafar, “wane ne maigidan naka?” Jaafar ya maida martani da cewa, “shugaban hukumar aikin Hajji.” wannan tattaunawar ta faru a ofishin Jaafar dake Wuye. A lokacin ne Jaafar ya kira shugaban hukumar aikin Hajji ta waya akan ya bashi dama ya lallashi IG Wala ya cire abinda ya wallafa. Sai dai IG Wala bai yarda ba duk da cewa bayan sun rabu, Jaafar ya kara kiran shi cikin dare.

Sakamakon abubuwan da suka guduna, CATBAN ta kaddamar da bincike game da bincike akan Jaafar da Daily Nigerian game da yunkurin bakanta mai girma sarkin Kano. Sakamakon binciken ya nuna cewa mai wallafa labarun na Daily Nigerian yana daga cikin wasu yan jaridu kimanin 43 da suke halarta da cin moriyar aikin Hajji kyauta wanda basu taba wallafa wani abu game da badakalar cin hanci da rashawa da ake yi a Hukumar aikin Hajjin ba.

Game da chakwakiyar Ganduje kuma, CATBAN ta yi kokarin gudanar da bincike ta hanyar jami’an gwamnati wadanda suke da kusanci da gwamna akan me ya sa za’ayi wannan bidiyo akan gwamna! Yawancin waÉ—anda muka tuntuba sun tabbatar da cewa an san Gwamnan da dabi'ar karban cin hanci. Wani jawabin da ya fito daga bakin dan gani kashenin Ganduje yana cewa, “a bar ma batun kama gwamna a bidiyo, Ganduje baya taba maida hannun kyauta baya (cin hanci).



Wani babban jami’in gwamnati a Kano ya bayyana cewa majigin gaskiya ne kuma akwai wani mutum da zai iya bayyana a gaban kwamitin da majalisar ta kafa, zai bada karin haske game da bidiyon.



CATBAN bata tsaya a nan ba, ta tsallaka har kan yan siyasar da suke ta aiki tukuru don siyasantar da, ko shashantar da lamarin. Daya daga cikin wadannan yan siyasa tuni yayi nisa wajen yin amfani da sunan shugaban kasa da fadar gwamnati don binne siyasar Ganduje. Ma'ana, sun riga sun tsayar da dan takara, zai yi murabus daga ofishin gwamnatin tarayya ya yi takara a madadin Ganduje. Tuni suka maye gurbinsa da wanda INEC ta riga ta rubuta.

Muna so mu jadda wadannan abubuwa:

- Majigin yana iya kasancewa gaskiya ko da ace kudi aka biya kafar watsa labaran ko wanda ya wallafa don cimma wata manufa ta siyasa.

- Jaafar Jaafar ya cancanci yabo a kowane irin hali ne amma ya kamata ya san illar shiga tsakanin irin wannan lamari.

- Ya kamata Gwamna Ganduje ya daure ya fadi gaskiya sannan yayi murabus a mutumce kafin ya makara.

- Majalisar jihar Kano zata iya yin amfani da wannan dama don cimma wata manufa ta kashin kai saboda makircin siyasa. Amma, ya kamata su gujewa hakan tunda yawanci sun yi ikirari kan cewa suna sane da dabi’un gwamnan amma basu da karfin zuciyar kai rahotonshi. Saboda haka dole su kasance masu adalci da gaskiya.

Karin bayani: Ma'anar CATBAN (Citizen Action to Take Back Nigeria), comrade IG Wala shine shugabanta.