Jam'iyyar APC ta ki mika sunan Senata Shehu Sani ga hukumar INEC.
A cikin wannan mako da muke ciki ne jam'iyyar APC mai mulki ta mikawa INEC sunan dukkan 'yan takararta a zaben 2019.
A wata sanarwa daga mai magana da yawun senatan ya fitar, an shaida ficewar shehu Sani daga jam'iyyar APC sakamakon rashin halacci da sukai masa.
Yace: "An yaudari senata Shehu Sani akan za'a bashi takara amma yanzu lokaci guda an mika sunan wani Uba Sani maimakonsa.
Idan baku manta ba tun lokacinda akai yayin sauyin sheka daga jam'iyya zuwa jam'iyya, aenata Shehu Sani yayi kudurin fita sabida rikici dake tsakaninsa da gomna Mallam Nasiru Elrufai. Shehu Sani yana cikin senatoci da jam'iyyar APC ta lallaba hatta shugaban kasa Buhari ma ya taimaka wajen shawo kan senatocin.
Tun kafin zaben fidda gwani gomnan jihar Kaduna ya nuna Mallam Uba Sani matsayin wanda zai tsayar takara senata a kaduna ta tsakiya saboda rikici dake tsakaninsa da Shehu Sani.
Haryanzu ba'a ji jam'iyyarda Shehu Sani zai koma ba yayinda magoya bayan senatan keta kiraye kirayen ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

