Sarkin Kano ya roki a dakatarda maganar videon Gomna Ganduje

Mai martaba sarkin kano Alh. Sunusi Lamido sunusi ya nemi alfarma a gidan Radio Freedom Kano su dakatarda bayanin faifen video nan da akace anga gomnan kano Abdullahi Ganduje yana karbar cin hanci miliyoyin daloli.

Faifen video ya fito ne daga hannun jaridar nan wacce mallakin haifefen jihar kano ce JAAFAR JAAFAR wanda ya kwarmatawa alumma irin badakalar kudi da gomnan yayi acikin videon.

Sarki Sunusi ya nemi alfarmar ne bisa ganin irin yadda tarzoma ka iya biyo bayan cigaba da fallasa abinda gomnan yayi acikin video.

Rokon sarkin ya isa hannun mai gabatarda shirin a gidan Radio Freedom wato shahararen dan jaridar nan Nasiru Salisu Zango wanda yayi kaurin suna wajen fallasa abubuwa da suka sabawa dokar kasa ko abubuwan cin amanar alumma.

A dokar gidan radio Freedom ko shugaban gidan baida hurumin hana a fallasa rashin gaskiar 'yan siyasa. Saidai wata majiya tace za'a iya karbar rokon sarkin saboda shi kadai ne yakeda damar ayi masa  irim wannan alfarma sai kuma wasu daidai kun malaman addini da sukeda mutunci a idon alummar jihar.

Zancen videon cin hanci da Ganduje ya karba na dalar Amurka milyan 5 yazama wani babban abin takaici a idon magoya bayansada alummar jihar Kano.