Jarumi Nura Hussain ya karyata videon Gomna Ganduje

Jarumin fina finan Hausa Nura Hussain ya karyata videon Ganduje da aka fitar.

Acikin wani gajeren video daya aika domin kare ubangidan nashi, jarumin yayi Allah wadai da videon da dan jarida Jaafar Jaafar ya fitar wanda aka nuna Gomna Ganduje yana karbar kudaden daloli.

Nura Hussain yace " Haba jaafar! Ya ina drama zakai min drama kodaye ba fanninka bane shiyasa kake ganin ba wanda zai gane. Ni wallahi da akacemin ga video anga kadimul islam yana karbar cin hanci har nace banida dan takara a jihar Kano ammasai gashi ka fitarda video da bashida maana kwata kwata. Na farko baka nuna mai bada kudin ba na biyu ka cire muryar videon lasanya wata sarewa. Wannan kudadenda kake magana sun kai dala milyan 5 to indai wabda aka nuna ne ko ni a kasuwancina ina juya kudinda suka kaisu bare gomna. Wai jaafar anya kasan dala milyan 5 kuwa a ido? Yakamata kome zakai kaji tsoron Allah kada ka dabawa kanka wuka. haba! Wai meke damunmu ne Hausawa duk kabilar kasarnan babu wadda take cin mutuncin shugabanninta sai mu. Meyasa?.

Saidai kuma bayan wannan martani da jarumin yayiwa dab jarida Jaafar Jaafar da kwana daya jaridar DailyNigerian da itace take watsa harkokin wannan badakala ta sake fitarda video na 2 kamar yadda ta fada cewa videos din sunkai 14 kuma duk a ofis din gomnan aka dauki bidiyon. Kuma videon na 2 yanada murya da komai ajiki.

Jaridar ta kuma fadi dalilinta na rashin saka murya a videon farko tace saboda bataso aji muryar wanda yadau bidiyon saboda sha'anin tsaro.

Yanzu haka dai majalissar jihar Kano ta nada kwamitin bincike don gano gaskiar lamarin videon da aka ga gomnan aciki. Idan har anyi nasarar tabbatarda videon to tabbas 'yan majalisun jihar zssu kada kuri'a don tsige gomnan jihar Abdullahi Ganduje.