Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta mikawa hukumar INEC sunayen dukkan 'yan takararta.
Jam'iyyar ta mika sunayen ne bayan kammala zabukan fidda gwani data gudanar a jihohin Nigeria.
Shugaban jam'iyyar Adams Oshiomole shine ya jagoranci mika sunayen.
Saidai a jihohi dayawa an samu kamarsu Kaduna, Adamawa, Zamfara akwai sauran rina a kaba saboda rikicinda ake tsakanin 'yan takarkarun senata da gomnonin jihohinsu.
A jihar Kaduna dai har yanzu ana kan rikicin dukda uwar jam'iyya ta kasa ta mika sunan Senata Shehu Sani dake wakiltar kaduna ta tsakiya, amma a bangaren gomnan jihar Mallam Nasiru Elrufai ke fafutukar lallai sai an baiwa Mallam Uba Sani takarar kujerar.
Hakazalika a jihar Zamfara ma uwar jam'iyya ta kasa bata goyi bayan wanda gomnan jihar Abdulaziz Yari ke muradin tsayarwa takarar gomna ba dukda rikice rikicenda akayi fama dashi a jam'iyyar wanda yayi sanadiyyar rasa wasu rayuka.

