Inuwa Yahaya ya lashe zaben fidda gwanin APC a Gombe


Alh. Inuwa Yahaya ya lashen zaben fidda gwanina gomna a jam'iyyar APC a Gombe da kuri'u masu rinye.

An gudanarda zaben fidda gwani matakin gomna a jam'iyyar APC wanda ya wakana babban dakin taro dake International Hotel dake fadar jihar Gombe.

An fara kada kuri'a ne da misalin karfe 3:00 na daren ranar lahadi 30/9/2018.

Ga sunayensu da kuri'arsu:
1- Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya: 859
2- Muhammad Jibril Barde: 463
3- Farouk Bamusa: 139
4- Barister Idris Umar: 68
5- Umar Kwairanga (Sarkin Fulani): 54
6- Alhaji Abubakar Habu Mu'azu: 49
7- Hon. Ibrahim Dasuki Jalo Waziri: 28
8- Hon. Khamisu Ahmad Mailantarki: 9
9- Aliyu Haidar: 5
Lalatattun Kuri'u: 44

Dukkan 'yan takarar sun bayyana cewa zasu marawa wanda yayi nasara acikinsu domin samun nasara a babban zabe dake tafe a 2019.