EFCC zata binciki shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomole

Babbar kotun kasa dake Abuja ta bada umarnin bincike kan tsohon gomnan jihar Edo wanda shine shugaban jamiyyar APC mai mulki a Nigeria.

Mai shari'a Anwuli Chikeire shine yabada umarnin bayan hukumar yaki da cin hanci ta (Anti-curruption crusader) wacce Bisho Osadolor Ochei yake shugabanta ta gabatarwa kotun takardar badalakar kudade da ake zargin tsohon gomnan yayi lokacinda yake rike da madafun iko.

Acikin takardar an bayyana cewa Adams Oshiomole yazama gomnan jihar Edo tun daga November 2011 zuwa November 2016. Kuma a karkashin gomnatin nasa ne aka karkatarda kudaden wadanda yawansu zai iya tafiyarda jihar na shekaru.

Bishop Ochei yace "Muna bukatar kotu ta bada damar a binciki tsohon gomnan sannan a gurfanar dashi domin hukunci. Munsha kaiwa EFCC kuka kan yadda Adams Oshiomole ya karkatarda kudaden amma bata maida hankali kan lamarin ba.

Ya zuwa yanzu dai na jiran matakinda hukumar EFCC zata dauka kan tsohon gomnan wanda ke shugaban jamiyyar APC.