Jagoran jam'iyyar APC a yankin kudu maso yamma Bola Ahmed Tinubu ya gana da buhari a yayinda ake gab da zaben fidsa gwani a jiharsa ta lagos.
Bola Tinubu yakai ziyarar ne domin neman mafita ga zaben fidda gwani saboda rikici da ya kunno kai tsakaninsa da gomna mai ci a jihar.
Bola Tinubu ya dage ne kan sai gomna AMBODE ya janye ya barwa SANWOLO sakamakon rashin biyayya da gomnan yake masa.
Haryanzu baa sasanta ba tsakanin Tinubu da gomnan saboda tirjiya da yayi cewa dole saidai APC ta bashi tiket.
Jihar lagos ta kasance jiha mai dumbin alumma saidai rikici siyasa yana neman raba kawunan manyan jihar.

