Boko haram sun hallaka Hauwa Liman

Kungiyar Jama'atu Ahlissunnah lida -da'awati wal-jihad (Boko Haram )ta hallaka wata membar kungiyar ceto ta RED Cross.

Hauwa Liman dai fitacciya ce a wajen ayyuka da kuma taimako abinda ya shafi kungiyar RED cross da suke zama a sansanonin 'yan gudun hijira a jihohin da ake fama da hare haren kungiyar Boko Haram.

Jaridar #TheCable ta ce Boko haram sun suna kokarin mayarda daya daga cikin 'yan matannan Leh Sharibu baiwa ta har abada.

A wani takaitacen video da Boko Haram suka fitar mai maganar yayi bayanin yadda suka durkusarda Hauwa kana daga bisani suka harbeta.

Mai maganar yace "Mun cika alkwarinda muka dauka na kashe daya daga cikin membobin kungiyar Red Cross ba'a binmu bashin alkawari.

Bayan Hauwa Liman da Boko haram suka hallaka akwai wata maaikaciyar asibiti Saifura Ahmed wacce takeda 'ya'ya biyu da kuma wata mai suna Luksha NGaddah sannan kuma sun hallaka wasu sojojin Nigeria guda 5.

Kungiyar Boko Haram dai sun dade suna addabar yankunan Arewa maso gabas Borno, Yobe, Adamawa. Mutane dubbai sun rasa ransu a sakamakon hare hare kuma har ila yau kungiyar bata gama dusashewa ba dukda dai sojojin Nigeria sun ci karfin kungiyar tun shekarar 2015 zuwa yanzu.