Banida wata alaka da videon Ganduje -Kwankwaso

Tsohon gomnan jihar Kano Senata Rabiu Musa Kwankwaso mai wakiltar Kano ta tsakiya ya musa zargin ake yayatawa cewa yanada hannu a fitarda videon con hanci na gomna Ganduje da jaridar DailyNigerian ta fitar.

Yayinda yake mayar da martani ga kwamishanan yada labaran jihar Kano, Malam Muhmmad Garba, inda yace mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar na aiki da yan adawa ne kuma makiyin jam’iyyar All Progressive Congress, APC ne, Kwankwaso ya ce bai da wata alaka da dan jaridan.

Senata Kwankwaso yace " Kowa dai yasan Jaafar Jaafar dan jarida ne mai zaman kansa. Kuma jaridar Daily Nigerian tashi ce kuma jarida ce mai zaman kanta.

"Bamu da wata alaka da wannan badakala kuma duk wanda yake zargin wani abu to yakawo hujja.

Martanin kwankwason ya fito ne ta hannun mai taimaka masa a harkar yada labarai wato Binta Spikin.

Bayan bayyanar videon badalakar kudaden ne kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba shine yayi zargin cewa dan jarida Jaafar Jaafar yana yiwa 'yan adawa aiki.