Senata Shehu Sani mai wakiltar kaduna ta tsakiya yayi Allah wadai da zaben fidda gwani na senatoci da aka gudanar a jihar Kaduna.
Bayanin ya fito ne daga hannun mai magana da yawun senatan.
Yace " Muna sanarda alumma cewa Senata Shehu Sani baya cikin wadanda aka gudanarda zaben fidda gwani dasu, kuma duk wanda yaje wurin a matsayin wakilin Shehu Sani to kowa ya sani bada yawun senatan yayi ba.
"Babbar jam'iyya ta kasa bata sanya wani lokaci na zaben fidda gwani ayau ba kuma mu bazamu amince da wannan karfa karfa ba.
Wannan ya biyo bayan rikici da ake kan wanda zai lashe zaben fidda gwanin tsakanin Shehu Sani da kuma Mallam Uba Sani da Gomna El-Rufai ke son a baiwa tiketin takarar.

