Sashin al'amuran shari'a na kasar Amurka sun karyata zarge zargenda akewa Atiku Abubakar.
Ma'aikatar shari'ar ta Amurka ta tabbatarda bata taba samun wata matsala da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ba. Biyo bayan jita jitar da ake yada cewa Amurka sun sanya masa takunkumi shiga kasar.
A cikin wani sakon email da shugaban sashin shari'a na Amurka Peter Carr ya turawa wakilin jaridar PUNCH.
Mr. Peter Yace " Nagode da kokarin bincike da jaridarku takeyi, a gaskia na bincika dukkan ajiyayun takardun laifi na kotunan Amurka, hakika babu wani suna Atiku Abubakar acikin kundin ajiyar laifuka na tsawon shekaru.
Bayanin ya fito ne bayan jaridar PUNCH din ta aikawa sashin shari'ar burutaniya sakon email don a bincika gaskiar labarinda ake alakantawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan cewa Amurka ta sanya masa takunkumi.
Tsohon shugaban kasar Nigeria Chief Olusegun Obasanjo ne ya fara fitarda zargin kan tsohon mataimakin nasa wanda hakan ya zama matsala tsakanin Atiku da wasu talakawa. Saidai kuma jama'a na mayarwa Obasanjon martani kan cewa karya yakewa Atiku tunda babu wata shaida watakila saboda sabanin ra'ayi ne ko kuma don Atikun yaki bashi kai ya juya shi.
Jita jita da jinginawa 'yan siyasa munanan kalmomi da zargi dai yazama ruwan dare a Nigeria musamman yadda 'yan siyasa ke amfani da zargin wasu mutane wajen cimma manufofinsu na siyasa.

