Shahararen jarumin fina finan Hausa Ali Nuhu ya samu shaidar digirin digirgir daga jami'ar ISM dake Cotonou a kasar Benin Republic.
An baiwa jarumin lambar girmawar ne duba da irin namijin kokarinsa kan bunkasa harkokin sana'o'i da yayi ta hanyar Kannywood da kuma kawo cigaba mai yawa ga rayuwar matasan Nigeria dama wasu kasashe makwabta.
Jami'ar ta karrama jarumin ne da shaidar digirin digirgir a fannin ilimin Falsafa wato "Doctorate degree "Philosophy" wanda yazama karin matsayin ga sunansa ya koma DR. ALI NUHU.
Manyan shuwagabannin jami'ar ne suka nazarta suka ga yadace su karrama Ali Nuhu. Sannan kuma daya daga cikin shugabanni a jami'ar wanda shine registra ADAMU WAKILI yace cancanta ce tasa suka zabi Ali Nuhu suka bashi wannan karramawa.
Yanzu haka dai masana'antar ta rude da murnar wannan karramwa, yayinda darktoci, furoduaoshi da jarumai maza da mata suke ta yayata hotunan karramawar a kafafen sada zumunta musamman Instagram.



