'Yan sanda sun cafke wani mutumda yayi 'Yarsa Mai Shekaru 13 Ciki A Garin Benin Dake Jihar Edo a nigeria
Mutumin mai suna Friday Moses, yanzu haka yana hannun jami'an 'yan sanda, inda ya bayyana cewa tun 'yar tasa na shekara bakwai a duniya ya soma lalata da ita, bayan mahaifiyarta ta rasu.
Yarinyar ta bayyana cewa mahaifinta yana zuwa gareta ne aduk lokacinda ya lura daga shi sai ita acikin gidan. Yana tilasta mata saduwa dashi aduk lokacinda ya bukaci mace koda bata so.
Friday wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa na yiwa 'yarsa ciki saidai ya nemi kotu tayi masa afuwar haka saboda shima ba son ransa bane sharrin shaidan ne
Shaidun gani da ido sun tabbatarda cewa Friday yana saduwa da diyar tashi kamar yadda ake zarginsa.
Yanzu haka dai ana cigaba da shariar, kafin daga bisani ta yanke masa hukunci daya dace dashi.

