An ceto gawar mutuminda ya fada tekun lagos

Mutumin wanda ba'a tabbatarda wanene ba, yayi tsalle ne tun daga babbar gadar nan  ya fada cikin tekun ruwan lagoon dake lagos. 

Jami'an ceto sun bayyana cewa anga sanda mutumin ya taho ya nufi Lagos island karshen babbar gadar kana daga bisani yayi tsalle cikin ruwan da misalin karfe 7:30 na safe. 

Tsallen mutumin cikin ruwa ya janyi hankalin masu wucewa bisa gadar har suka tsaya domin sanarda masu ceto abinda yake faruwa. 

Wani shaidar gani da ido yace"An samu nasarar ceto gawar mutumin wanda ba'a san dalilinda yasa ya aikata haka ba, saidai kuma saboda yadda ya jikkata an cetoshi ne lokacin rai yayi halinsa. 

Jami'an ceton sun kara da cewa bayan an sanar dasu sunyi iya kokarinsu tareda hadin gwiwar direbobin dake kusa domin ceto shi amma bayan an fito dashi aka samu  yazama gawa.



har Yanzu ba'a tabbatarda wanene ba