Kamfanin shirya fina finan Hausa "Sheshe Movies" ya biya jarumi Ali Nuhu 500,000 domin ya aske gashin kansa.
Kamfanin ya biya jarumin ne a yayinda yake daukar wani sabon fim mai suna "KAZAMIN SHIRI".
Ma shirya shirin sun bayyana cewa Ali Nuhu babban jarumi ne wanda bazai yiwu ace yayi aski haka kurum ba saboda yadda yake fita kasashe daban daban kuma yana matukar alfahari da kwalliya da gashin nasa.
Fim din "Kazamin Shiri" fim ne da aka shirya kuma yana daukeda manyan jarumai maza da mata wadanda zasu taka rawa a fanni daban daban na cikin shirin.
Shahararen Furodusan nan ALH. sheshe shine ya shirya fim din kuma yadau nauyin shirya babban fim din.
Wannan dai shine karo na farko da wani kamfani ya viya irin wannan makudan kudade domin jarumi yayi aski. Saidai watakila hakan bazai yiwa wasu furodusoshi dadi ba saboda gudun kar sauran jarumai suce suma sai an biyasu idan hakan ta taso.

