Daruruwan mabiya akidar shi'a sunyi zanga zangar a saki malaminsu Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda yacika kwanaki dubu daya 1000 a hannun jami'an tsaro.
Manyan malaman shi'a dayawa sun halarci zanga zangar da aka gudanarda ita tun daga kasuwar wuse market zuwa sakateriyar gomnatin tarayya dake babban birnin tarayya Abuja.
An rufe zakzaky ne tareda matarsa da kuma wasu mabiyansa sakamakon wata hatsaniya da ta taba barkewa tsakaninsu da sojojin Nigeria a lokacinda shugaban sojin Tukur Yusuf Buratai zai wuce a bisa wata hanya da yan shiar suka toshe don gudanarda wani taron addini da sukeyi.
A kalla mutane 300 ne suka hallaka a wancan rikicin wanda ya jawo sanadiyyar dakushewar kaifin akidar shi'a a Nigeria.
A baya ma mabiyan shi'a sun sha zanga zangar a sake malamin nasu saidai har yau gomnati batayi wani yunkurin sakeshi ba dukda wata kotu ta bayarda belinsa a shekarar bara.

